17 Nuwamba 2020 - 13:45
​Iran: Dukaknin Kalaman Batanci Na Sarkin Saudiyya A Kan Iran Maimaici Ne

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ne ya bayyana hakan a yau a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Tehran, inda ya ce babu wani abu sabo da sarkin masarautar ta al Saud ya fada dangane da siyasar kasarsa a kan kasar ta Iran.

ABNA24 : Ya ci gaba da cewa, har kullum kalaman batunci ba za su taba zama hanyar warware matsaloli da cimma buri ba, yin aiki tare da girmama juna shi ne hanya mafi dacewa wajen samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya.

Kasashen da suke tunanin cewa za su iya sayen tsaro daga waje, ko kuma za su mayar da daukacin yankin karkashin ikonsu da kuma yin abin da suka ga dama ta hanyar sayen manyan makamai daga Amurka, zaton cewa makaman Amurka ne za su kare kujerunsu na sarauta, to suna tafka babban kure.

Daga karshe ya ce Iran din tana nan kan bakanta na kyautata alaka da kowace kasa a yankin gabas ta tsakiya, daga ciki kuwa har da kasar Saudiyya matukar dai tana bukatar hakan.

342/